logo

HAUSA

Gamayyar kasa da kasa sun taya kasar Sin murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS

2021-06-23 13:31:22 CRI

Gamayyar kasa da kasa sun taya kasar Sin murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS_fororder_hoto-JKS

Kwanan baya, gamayyar kasa da kasa sun taya kasar Sin murnar cika shekaru 100 da kafuwar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin wato JKS, jami’an jam’iyyun siyasa da na majalisar kafa dokoki na wasu kasashe 24, sun nuna yabo matuka kan manyan nasarorin da JKS ta cimma. Suna mai imanin cewa, tabbas, jam’iyyar JKS za ta bude wani sabon shafi mai kyau bisa jagorancin shugaban kasar Sin Xi Jinping.

Shugaban Jam’iyyar Jubilee ta kasar Kenya, kana shugaban kasar Uhuru Kenyatta ya mika sakon taya murna ga takwaransa na kasar Sin Xi Jinping da kuma dukkanin al’ummomin kasar Sin, ya ce, kasar Sin ta cimma burin kawar da talauci kafin shekaru 10 da aka tsara bisa jadawalin neman dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 da MDD ta tsara, wannan abin koyi ne ga kasa da kasa. Hakika, bisa jagorancin JKS, al’ummomin kasar Sin za su kara hadin gwiwa domin gina al’umma mai wadata.

Shugaban jam’iyyar dimokuradiyya ta jama’ar kasar Tajikistan, kana shugaban kasar Emomali Rahmon ya nuna kyakkyawan fatansa ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, da dukkanin al’ummomin kasar Sin, inda ya ce, bisa jagorancin JKS, ko shakka babu, jama’ar kasar Sin za su ci gaba da inganta bunkasuwar tattalin arzikin kasar, da ba da karin gudummawa ga bunkasuwar kasa da kasa cikin lumana. (Maryam)