logo

HAUSA

Sin ta bukaci kasashen da abin ya shafa da su magance matsalar keta hakkin dan-Adam

2021-06-23 09:33:29 CRI

Sin ta bukaci kasashen da abin ya shafa da su magance matsalar keta hakkin dan-Adam_fororder_zhao

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bukaci kasashen da abin ya shafa, da su dauki managartan matakai don magance manyan matsalolinsu na take hakkin bil-Adama.

Zhao Lijian ya yi wannan kira ne, bayan wata sanarwa da kasar Canada ta fitar a madadin wasu kasashen yamma, inda a cikinta ta zargi kasar Sin game da batutuwan da suka shafi yankunan Xinjiang da Hong Kong, da kuma Tibet na kasar Sin.

Kakakin ya ce, manufar wadannan kasashe, ita ce mayar da kasar Sin saniyar ware, da neman hana ci gabanta. Sai dai yayin da wadannan kasashe ke ikirarin martaba kare hakkin bil-Adama a kasashensu, a hannu guda kuma sun kauda kai game da munanan matsalolinsu na kare hakkin bil-Adama, inda ya ba da misali da yadda kasashe kamar Canada, da Amurka, da Burtnaiya ke yawaita keta hakkin bil-Adama.

A don haka, jami’in na kasar Sin ya bukaci wadannan kasashe, da su kalli kansu, su dauki matakan da suka dace wajen magance matsalolinsu na kare hakkin bil-Adama, su martaba ka’idoji da dalilai da suka kai ga kafa dokokin MDD, da muhimman ka’idojin hadin gwiwar kasa da kasa, su kuma aikata abin da ya dace a zahiri, don ganin an samu ci gaban da ya dace a kokarin da ake yi na kare hakkin dan-Adam.(Ibrahim)