logo

HAUSA

Darektan AHF: Boye alluran COVID-19 yana gurgunta aikin yaki da annobar a duniya

2021-06-23 09:52:02 CRI

Darektan AHF: Boye alluran COVID-19 yana gurgunta aikin yaki da annobar a duniya_fororder_疫苗-3

Darektan gidauniyar yaki da cutar kanjamau dake kasar Kenya (AHF) Samuel Kinyanjui, ya dora alhakin tafiyar hawainiyar da ake samu a kokarin da ake yi na dakile cutar COVID-19 a nahiyar Afirka, kan halayyar wasu kasashe masu wadata na boye alluran rigakafin.

Jami’in ya ce, yadda irin wadannan kasashe suke boye rigakafin, ya haddasa karancin magungunan ceton rayuka a nahiyar, abin da ya sa ake ganin, karuwar masu kamuwa da cutar ke barazana ga tsarin kiwon lafiyar al’umma.

A don haka, ya bukaci kasashe masu karfin tattalin arziki, da su raba alluran rigakafin, su cire batun ‘yancin mallakar fasahar samar da alluran, su kuma taimaka wajen kafa kamfanonin samar da rigakafin a Afirka.

Alkaluman da cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afirka(Africa CDC) ta fitar, sun nuna cewa, ya zuwa ranar 14 ga watan Yuni, an yiwa mutane miliyan 42.1 allurar a nahiyar, yayin da kaso 0.79 na al’ummar nahiyar ce kadai suka karbi cikakkiyar alluran.

Kasashen nahiyar da ke kan gaba a fannin yiwa al’ummominsu rigakafin, sun hada da Morocco, da Masar, da Najeriya, da Habasha, da Afirka ta kudu. Hakan ya samu ne, saboda managarcin tsari, da yadda ake raba rigakafin, da kuma horas da ma’aikatan lafiya.(Ibrahim)