Kasar Sin ta yi kira ga Canada da ta dakatar da keta hakkokin ‘yan asalin kasar
2021-06-23 20:45:17 CRI
Minista a ofishin tawagar kasar Sin da ke ofishin MDD dake birnin Geneva,Mr.Jiang Duan, yayi kira ga kasar Canada, da ta gaggauta dakatar da keta hakkokin ‘yan asalin kasar, kana hukumar kare hakkin bil adama ta MDD, ta bi kadin halin da ake ciki game da keta hakkin bil adama a Canada.
Jiang Duan, wanda ya yi wannan kira a jiya Talata, yayin zama na 47, na hukumar kare hakkin bil adama ta MDD, ya ce ya yi matukar damuwa game da munin halin da ake ciki, na keta hakkokin bil adama a Canada.
Don haka a madadin kasashe da dama ya bayyana cewa, tarihi ya shaida yadda Canada ta rika korar ‘yan asalin kasar daga filayen su, ta hallaka wasu, kana ta batar da al’adun su. Har ila yau duniya ta kadu, da jin yadda aka gano kabarin wasu yara ‘ya’yan ‘yan asalin kasar su sama da 200 a wata makarantar kwana dake Canada.
Minista Jiang ya kara da bayyana matukar damuwa, game da yadda a cewarsa, gwamnatin Canada ke nuna wariya, tare da muzgunawa ‘yan ci rani a wasu cibiyoyinta na tsare bakin haure. Ya ce tsakanin shekarun 2006 zuwa 2014 kadai, Canada ta tsare dubban ‘yan ci rani ba tare da yi musu shari’a ba.
Daga nan sai Jiang ya bukaci hukumar kula da hakkin bil adama ta MDD, da ofishin babban kwamishinan MDD mai lura da hakkokin bil adama, da ma sauran sassa masu ruwa da tsaki, da su sanya ido kan yanayin kare hakkokin bil adama a kasar Canada. (Saminu)