logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD: Ya kamata kasashen duniya su ba da gudunmawa wajen ingiza shimfida zaman lafiya a Afghanistan

2021-06-23 13:16:01 CRI

Zaunannen wakilin Sin dake MDD Zhang Jun ya bukaci kasashen duniya da su ba da cikakiyar gudunmawa, wajen ganin an ingiza shimfida zaman lafiya a Afghanistan. Zhang Jun ya bayyana haka, yayin taron kwamitin sulhu na MDD kan batun Afghanistan ta kafar bidiyo,.

Ya ce, yanzu Afghanistan na cikin wani muhimmin lokaci, wato ba a iya samun tabbaci ba a kasar. Bayan da kasar Amurka ta yi shela a tsakiyar watan Afrilu na bana, cewar za ta fara janye sojojinta daga Afganistan a bana, an samu koma baya a shawarwarin neman sulhu da ake yi tsakanin bangarori daban daban na Afghanistan. Sakamakon haka, yanayin tsaro da tattalin arziki da na jin kai da ake ciki a kasar sun kara tsananta. Wannan ya sa bangaren Sin ya damu sosai kan halin da ake ciki a kasar.

Zhang Jun ya ce, makomar Afghanistan na cikin hannun jama’arta, a don haka, jama’a za su zabi hanyar da za su bi nan gaba. Ya kamata, kasashen duniya su bar jama’ar Afghanistan su tafiyar da harkokin kasarsu da kansu, su ba da gudunmawa wajen ingiza shimfida zaman lafiya da sulhu a kasar. A wani bangare kuma, ya kamata bangarori daban-daban na Afghanistan, su dora muhimmanci kan muradun kasar da jama’arta, don tabbatar da ci gaban da aka samu a cikin shekaru 20 da suka gabata, da bullo da wata hanyar da ta dace da halin da kasar ke ciki.

Zhang ya kara da cewa, a cikin wasu lokuta masu zuwa, batun janyewar sojojin ketare daga kasar, zai yi tasiri matuka ga halin da kasar ke ciki. Sabo da haka, bangaren Sin ya nemi a janye sojojin ketare daga Afghanistan bisa shiri. Har ma ya kamata a yi cikakken shawarwari da gwamnatin kasar Afghanistan kan matsalolin da za su bullo bayan janyewar sojojin ketare. Bugu da kari, ya kamata su da sanar wa sauran kasashen dake yankin bayanai game da shirinsu yadda ya kamata, domin kokarin magance lalacewar yanayin tsaro a shiyyar. (Amina Xu)