logo

HAUSA

Jakadan Amurka dake Rasha zai koma Moscow cikin wannan mako

2021-06-22 11:01:40 CRI

Jakadan Amurka dake Rasha zai koma Moscow cikin wannan mako_fororder_hoto

Jiya Litinin, kakakin majalisar gudanarwar kasar Amurka Ned Price ya bayyana cewa, jakadan kasar Amurka dake kasar Rasha John Sullivan zai koma birnin Moscow, fadar mulkin kasar Rasha cikin makon nan. Ya ce, kasar Amurka tana kokarin bude hanyoyin mu’amala a tsakaninta da kasar Rasha, domin kare moriyar kasar Amurka da kuma sassauta kalubalolin da za su haddasa sabani a tsakanin kasashen biyu.

Haka kuma, ya yi maraba da dawowar jakadan kasar Rasha dake kasar Amurka Anatoly Antonov, birnin Washington, fadar mulkin kasar Amurka.

A ranar 16 ga wata, yayin ganawarsu a birnin Geneva na kasar Switzerland, shugabannin kasashen Amurka da Rasha sun cimma matsayi daya kan dawowar jakadunsu wuraren aikinsu. Rahotanni na cewa, Anatoly Antonov ya riga ya fara aiki a birnin Washington tun a ranar 20 ga wannan wata. (Maryam)