logo

HAUSA

Sin ta yi watsi da kalaman babban kwamishinan MDD game da Hong Kong da Xinjiang

2021-06-22 21:20:18 CRI

Sin ta yi watsi da kalaman babban kwamishinan MDD game da Hong Kong da Xinjiang_fororder_26e88f7ce4fe4c97bf6f5af70b60a694

Kakakin ofishin zaunannen wakilin Sin a ofishin MDD dake Geneva na kasar Switzerland da sauran kungiyoyin kasa da kasa Liu Yuyin, ya ce kalaman da babban kwamishinan MDD mai lura da kare hakkin bil adama ya yi, dongane da yankin Hong Kong da jihar Xinjiang, ba sa kan turba, sun kuma sabawa hakikanin halin da yankunan 2 ke ciki. A hannu guda kuma, hakan tsoma baki ne a harkokin cikin gidan kasar Sin.

Liu ya ce "Ina son kara jaddada cewa, Hong Kong da Xinjiang bangarorin Sin ne da ba za a iya balle su ba. Kuma harkokin yankin HK da jihar Xinjiang, sun shafi kasar Sin kadai, ba sa bukatar tsoma bakin wani bangare daga wajen kasar. Kaza lika Sin na tsayawa tsayin daka wajen kare ‘yancin kai, da tsaro da moriyar ci gaban ta, tana kuma adawa da duk wani mataki na tsoma mata baki a harkokin gidan ta.

Sin ta yi watsi da kalaman babban kwamishinan MDD game da Hong Kong da Xinjiang_fororder_微信图片_20210622211933

A wani ci gaban kuma, kasar Belarus ta gabatar da bayanin hadin gwiwa, a madadin kan ta da wasu karin kasashe 65, inda a cikin sa ta jaddada cewa, martaba ‘yancin kai da kare martabar yankunan kasashen duniya, ba tare da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe masu mulkin kansu ba, matakin da hadakar kasashen suka ce jigo ne, na wanzuwar alakar kasa da kasa.

Kasar Sin dai ta jima tana bayyana cewa, harkokin Hong Kong da jihar Xinjiang, da Tibet, harkoki ne na cikin gidan kasar Sin, kuma bai dace kasashen ketare su tsoma baki cikin su ba.

Baya ga wannan bayanin hadin gwiwa na wasu kasashe, akwai kuma kasashe 6 mambobin kungiyar GCC, wadanda suka aike da wasikar mara baya ga manufar ta kasar Sin. Har ila yau, akwai karin wasu kasashe sama da 20 da suke shirin nuna goyon bayan Sin, ta cikin wasu daidaikun sanarwa.

Yanzu haka dai adadin sassa sama da 90 sun riga sun bayyana fahimtarsu da goyon baya ga matsayar da Sin ta dauka. (Saminu)