logo

HAUSA

Amurka tana shirin kakabawa Rasha sabbin takunkumai kan zargin sanyawa Navalny guba

2021-06-21 13:59:07 CRI

Amurka tana shirin kakabawa Rasha sabbin takunkumai kan zargin sanyawa Navalny guba_fororder_210621-Ibrahim04-Amurka da Rasha

Mashawarcin Amurka kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya bayyana a jiya Lahadi cewa, Amurka tana shirin kakabawa Rasha wasu karin sabbin takunkumai, kan zargin da ake mata na sanyawa Alexei Navalny, mai suka gwamnatin Rasha guba.

Sullivan ya bayyana haka ne, yayin wata zantawa da gidan talabijin na CNN, yana mai cewa nan ba da dadewa ba, Amurkar tana shirin kakabawa Rasha sabbin takunkumai kan wannan batu, don tabbatar da cewa, takunkuman sun kai ga sassan da suka dace. Daga nan kuma, Amurkar za ta kara sanya takunkumai kan makamanta masu guba.

Kalaman Sullivan na zuwa ne, ’yan kwanaki bayan da shugaba Joe Biden ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a Geneva na kasar Switzerland, ganawa ta farko tsakanin shugabannin biyu, tun bayan da Biden ya kama aiki.

A watan Maris ne, gwamnatin Biden ta sanar da kakkaba jerin takunkumai da haramci kan wasu ’yan kasar Rasha da hukumominta, bisa zargin da ake mata na sanyawa Navalny guba. (Ibrahim)