logo

HAUSA

Masar ta gabatar da korafi ga MDD game da matakin kashin kai da Habasha ta dauka na gina dam a kogin Nile

2021-06-13 15:45:18 CMG

Masar ta gabatar da korafi ga MDD game da matakin kashin kai da Habasha ta dauka na gina dam a kogin Nile_fororder_0613-Masar-ahmad

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta sanar cewa kasar ta aike da wasika ga kwamitin sulhun MDD dake tabbatar da cikikkiyar kin amincewarta da matakin kashin kai da Habasha ta dauka na gina madatsar ruwa ta (GERD).

A cewar sanarwar ma’aikatar, wasikar wacce aka aika a ranar Juma’a an zargi kasar Habasha da yunkurin lalata kokarin da ake na neman cimma yarjejeniyar kasashe uku game da dokokin dake shafar aikin cike kogin da kuma aikin gina madatsar ruwa da yunkurin tursasawa kasashen biyu dake makwabtaka da teku wato kasashen Masar da Sudan ta hanyar daukar mataki na kashin kai wanda hakan karara ya sabawa dokokin kasa da kasa.

Kasar Habasha ta tsara yin gaban kanta wajen cigaba da zagaye na biyu na aikin gina madatsar ruwan GERD a watan Yuli, yayin da kasashen Masar da Sudan ke nuna damuwa cewa matakin zai iya shafar albarkatun ruwan da suke amfani da shi daga tekun Nile.

A makon jiya, ministan albarkatu na kasar Masar, Mohamed Saafan, ya bayyana ta kafar bidiyo a taron tattaunawar kungiyar kwadago ta kasa da kasa , cewa daukar matakin bangare guda da kasar Habasha ta yi na aikin gina madatsar ruwan ba tare da yarjejeniyar amincewa a tsakanin bangarorin ba zai yi matukar haifar da illa ga fannin aikin gona ga kasashen biyu dake makwabtaka da kogin.(Ahmad)

Ahmad