logo

HAUSA

Giwayen Sin masu kaura sun dan yada zango a wani gari a kudu maso yammacin kasar

2021-06-11 10:15:34 CRI

Giwayen Sin masu kaura sun dan yada zango a wani gari a kudu maso yammacin kasar_fororder_7dd98d1001e93901e6434e695875c8ef37d19642

Garken giwayen Asiya wadanda kaurarsu ta dauki hankalin kasa da kasa sun yanke kudirin dan yada zango a garin Shijie dake birnin Yuxi, a lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, hukumomin kasar sun tabbatar da hakan a jiya Alhamis.

Wani namijin giwa, wanda ya fice daga cikin garken kwanaki biyar da suka gabata, yanzu yana da kusan nisan kilomita 11.8 daga dajin Anning, wani gari ne a karkashin ikon Kunming, babban birnin lardin. Dukkan giwayen suna cikin koshin lafiya da tsaro, kamar yadda hedkwatar dake sa lura kan kaurar giwayen ta bayyana.

Kimanin wata guda ke nan, hukumomin kasar Sin suka tura jami’an ‘yan sanda domin yiwa garken giwayen rakiya, tare da share musu hanyoyin mota don su samu damar wucewa kana jami’an na ajiye abinci domin dauke hankalin giwayen don kaucewa shiga yankunan dake da cunkoson jama’a.

Nau’in Giwayen na Asiya suna karkashin kulawar kasar Sin a mataki na A, inda galibi ake samunsu a lardin Yunnan. Bisa namijin kokarin da ake yi wajen ba su kariya, a yanzu haka, adadin giwayen dajin da yawansu ya karu zuwa kusan 300, daga adadin 193 a shekarun 1980.(Ahmad)