logo

HAUSA

Fasahar saka darduma na kabilar Tibet na taimakawa wajen raya kauyukanta

2021-06-09 13:41:05 CRI

Fasahar saka darduma na kabilar Tibet na taimakawa wajen raya kauyukanta_fororder_1

Dardumar kabilar Tibet, tana maganin sanyi sosai ga makiyaya a wuraren dake da tsayi matuka. Tana kuma da tarihin fiye da shekaru 3000, ana kuma amfani da ita a harkokin yau da kullum, ana kuma zauna a kanta da safe, bayan zama abin rufewa kamar bargo da dare, yayin da ake sanya karamar dardumar a kan sirdi.

Kamfanin Shengyuan na samar da darduma na birnin Xining dake lardin Qinghai ya samar da irin wannan dardauma ta hanyar amfani da ulu na Tibet mai inganci da ake samu a wannan wuri, don yayata al’adun kabilar Tibet da raya sha’anin kauyuka. (Amina Xu)