logo

HAUSA

Gwamnatin Nijeriya: Dakatar da Twitter ya dace da muradun kasar

2021-06-08 12:26:14 CMG

Gwamnatin Nijeriya: Dakatar da Twitter ya dace da muradun kasar_fororder_twitter

Ministan kula da harkokin wajen Nijeriya Geoffrey Onyeama, ya ce dakatar da kafar sada zumunta ta Twitter a kasar, ya dace da muradun kasar ta fuskar tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Geoffrey Onyeama ya bayyana haka ne a jiya, lokacin da yake wata ganawar sirri da jakadun kasashen Amurka da Birtaniya da Canada da Ireland da kuma Tarayyar Turai.

Ya kuma shaidawa manema labarai cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari na da burin tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasar da al’ummarta, kuma gwamnati na goyon bayan amfani da dandamalin sada zumunta ta hanyar da ta dace, wato ta yadda ba za su yi barazana ga tsaro da hadin kan kasar ba.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, gwamnatin Nijeriya ta ce ta dakatar da ayyukan Twitter a kasar, kwanaki biyu bayan kafar ta cire wani sako da shugaban Buhari ya wallafa, inda ya gargadi ‘yan aware game da kai hare-hare kan gine-ginen gwamnati. (Fa’iza Mustapha)

Faeza