Yawan mutanen da suka mutu a hadarin jirgin ruwan Najeriya ya kai 76
2021-05-30 15:51:45 CRI
Hukumomi a Najeriya sun bayyana cewa yawan mutanen da suka mutu a sanadiyyar kifewar jirgin ruwan da ya afku a ranar Laraba a Kogin Neja a arewacin Najeriya ya karu zuwa 76 ya zuwa ranar Juma’a.
A wata sanarwa, Yahaya Sarki, kakakin gwamnan jahar Kebbi Atiku Bagudu ya sanar da jami’an ‘yankin cewa, an gano gawarwaki 76 ya zuwa yanzu, wadanda suka mutu sakamakon kifewar jirgin ruwa wanda an yi amanna ya faru ne a sanadiyyar daukar fasinjojin da suka wuce kima yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wata kasuwa a jahar Kebbi da suka taso daga wani kauyen jahar Naija dake makwabtaka da jahar a ranar Larabar da ta gabata.
Sanarwar tace an samu nasarar ceto sama da mutane 20 da ransu, kuma har yanzu ana cigaba da gudanar ayyukan ceton.
A cewar sanarwar, gwamna Bagudu yayi kira ga al’umma musamman masu ta’ammali da jiragen ruwa da fasinjoji dasu koyi darasi daga abubuwan da suka faru kana su guji jefa rayuwarsu cikin hadari.
Bagudu ya ce, gwamnatinsa zata yiwa dokokin sufuri ta ruwa kwaskwarima domin kaucewa sake fuskantar hasarar rayuka da dukiyoyi a nan gaba.(Ahmad)