logo

HAUSA

Sin na fatan tsagin Amurka zai aikata abin da yake furtawa tare da kauracewa kulla makarkashiya

2021-05-11 20:46:13 CRI

Sin na fatan tsagin Amurka zai aikata abin da yake furtawa tare da kauracewa kulla makarkashiya_fororder_微信图片_20210511214148

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce kamata ya yi Amurka ta rika aikata dukkanin abubuwan da take fadi, tare da kauracewa kulla makarkashiya, ita da wasu ‘yan kanzaginta.

Kalaman na Hua, martani ne ga kalaman sakataren wajen Amurka Antony Blinken, wanda a kwanakin nan aka jiyo shi yana cewa, bangaren Amurka zai sauke dukkanin nauyin dake wuyansa, game da cudanyarsa da sauran sassa.

Blinken wanda ya yi wannan tsokaci, yayin taron koli na kwamitin tsaron MDD game da martana cudanyar dukkanin sassa, da girmama tsarin kasa da kasa karkashin inuwar MDD dake matsayin jigo, ya ce a ‘yan shekarun nan, wasu matakai da kasar sa ta aiwatar, sun gurgunta tsarin gudanar da al’amura a matakin kasa da kasa, don haka a yanzu Amurka za ta dukufa wajen shiga a dama da ita, a dukkanin cudanyar hukumomi na sassan kasa da kasa yadda ya kamata.  (Saminu)