logo

HAUSA

Kamata ya yi Sin da Amurka su yi takara mai tsafta

2021-05-11 20:57:26 CRI

Kamata ya yi Sin da Amurka su yi takara mai tsafta_fororder_微信图片_20210511214208

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta ce idan har Sin da Amurka na da burin yin takara da juna, to kamata ya yi su yi hakan bisa adalci, tare da kiyaye ka’idojin kasuwa.

Hua wadda ta bayyana hakan a Talatar nan, ta ce tun da jimawa Amurka ke bayyana Sin a matsayin muhimmiyar abokiyar takarar ta, don haka a matsayin Amurka na kwararriyar ‘yar wasa mai karfin gaske, kamata ya yi a ce ta fahimci dabaru na hanzari, na koli dake da matukar tasiri a takara.

Kuma tun da burin abokan takara shi ne ci gaba da samun gogewa, tare da samun karin sakamako, bai kamata a buge da ture juna, ko nuna kin jinin sauran abokan takara ba, duba da cewa yin hakan ba zai haifar da komai ba, sai fuskantar horo na kora daga filin wasa. (Saminu)