logo

HAUSA

Kasashen Botswana da Zambia sun bude gadar Kazungula

2021-05-11 10:30:28 CRI

Kasashen Botswana da Zambia sun bude gadar Kazungula_fororder_210511-Kazungula bridge

A jiya ne kasashen Botswana da Zambia, suka kaddamar da gadar Kazunguka cikin hadin gwiwa, gadar da ta kunshi hanya da layin dogo da ya ratsa ta kan kogin Zambezi da suka hade kasashen biyu da kuma wata tashar kan iyaka.

Ana sa ran gadar mai tsawon mita 923, wadda ta lashe tsabar kudi har dalar Amurka miliyan 259.3, za ta saukaka shiga kasuwannin kasa da kasa, ta hanyar hadewa da manyan tashoshin ruwa da kuma kara inganta kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (SADC).

A jawabinsa yayin bikin, shugaban kasar Botswana Mokgweetsi Masisi ya bayyana cewa, gadar Kazungula, za ta taimaka wajen inganta cinikayya, da samar da ayyukan yi, da fadada harkokin tattalin arziki a kasashen SADC. Za kuma ta hanzarta shirin dunkulewar shiryyar kudancin Afirka yadda ya kamata.

An dai fara aikin gina gadar ce a shekarar 2014, ana kuma sa ran tashar kan iyakar ta rika aiki na sa’o’i 22 a kowace rana. (Ibrahim)