logo

HAUSA

Shugaban Nijeriya ya bukaci a tabbatar da kiyaye dokokin sufurin ruwa

2021-05-11 09:35:54 CRI

Shugaban Nijeriya ya bukaci a tabbatar da kiyaye dokokin sufurin ruwa_fororder_尼日利亚总统-buhari

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya yi kira ga hukumomin sufuri na kasar, su tabbatar da kiyaye dokokin sufurin hanyoyin ruwa, a matsayin hanyar kaucewa hadduran kwale-kwale a nan gaba.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake jimamin mutuwar wasu mutane sanadiyyar hatsarin kwale-kwale a jihar Niger dake arewa maso tsakiyar kasar, a karshen makon jiya.

Shugaban ya bayyana matukar jimamin dangane da aukuwar lamarin, yana mai jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka jikkata.

Shugaban ya kuma yabawa ayyukan masu aikin ceto da masu ninkaya, inda ya bukaci a dauki darasi daga lamarin domin kaucewa sake aukuwar makamancinsa a nan gaba.

Kawo yanzu, an ceto mutane 65 yayin da ake ci gaba da aikin ceton don gano wadanda suka bace. (Fa’iza Mustapha)