logo

HAUSA

An kammala baje kolin hajojin sayayya na kasa da kasa a Hainan

2021-05-10 20:28:57 CRI

An kammala baje kolin hajojin sayayya na kasa da kasa a Hainan_fororder_42166d224f4a20a48547ced7a626e22a730ed0c6

A yau Litinin ne aka kammala baje kolin kayayyakin sayayya na kasa da kasa karo na farko da kasar Sin ta shirya, a Haikou na lardin Hainan dake kudancin kasar.

Baje kolin na kwanaki 4 ko CICPE a takaice, ya samu halartar wakilai daga kasashe da yankuna 70, yayin da kamfanoni 1,505 na gida da na wajen kasar Sin suka hallara.

Bugu da kari, baje kolin ya samu halartar baki sama da 240,000, yayin da fadin wurin baje kolin ya kai sakwayamita 80,000. Shi ne kuma irin sa na farko da ya karkata ga baje hajoji mafiya inganci a matakin kasa, kamar dai yadda mashirya bikin suka bayyana.  (Saminu)