logo

HAUSA

Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta tallafawa Indiya yaki da COVID-19

2021-05-10 10:51:05 CRI

Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta tallafawa Indiya yaki da COVID-19_fororder_210510-red cross of China

Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta baiwa Indiya tallafin dala miliyan 1 na tsabar kudi domin taimaka mata a yaki da annobar COVID-19, hukumar agajin ta (CRCF) ta sanar da hakan a jiya Lahadi.

Bugu da kari, gudunmawar kayayyakin aikin yaki da annobar wanda kungiyar agajin ta samar tuni sun bar garin Chengdu dake lardin Sichuan a kudu maso yammacin kasar Sin tun a safiyar ranar Lahadi zuwa garin Bangalore na kasar Indiya, a cewar CRCF.

CRCF ta bayyana cewa, kayayyakin sun hada da na’urar samar da iskar oxygen guda 100, da na’urar taimakawa numfashi da ake daurawa fuska guda 20, da wasu nau’ikan na’urorin numfashi na ventilators guda 20. (Ahmad)