logo

HAUSA

Sin tana fatan dukkan bangarori za su goyi bayan cudanyar sassa daban-daban

2021-05-07 19:21:11 CRI

Sin tana fatan dukkan bangarori za su goyi bayan cudanyar sassa daban-daban_fororder_汪文斌-1

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana cewa, kasarsa tana fatan yin aiki da dukkan bangarori, domin nanata goyon bayanta ga cudanyar sassa daban-daban da kare martabar tsarin kasa da kasa da MDD ke jagoranta.

Kalaman nasa na zuwa ne, yayin da kasar ta Sin ta karbi shugabancin karba-karba na kwamitin sulhun MDD na watan Mayu. Ya ce, bikin baje kolin kayayyakin sayayya na kasa da kasa na farko da kasar Sin din take gudanarwa kamar yadda aka tsara, ya nuna kudurin kasar da imanin da ta ke da shi, na kara bude kofarta ga kasashen waje.

Wang ya kuma gabatar da nasarar da kasar ta cimma na sake harba rokar Long March 5B sararin samaniya. Yana mai cewa, nau’in rokar yana da wani fasali na musammam, kuma gabilin sassansa za su narke su kuma baje a cikin iska, kana yiwuwarsu ta haddasa wata illa ga ayyukan jiragen sama da ma kasa kadan ne sosai. (Ibrahim)