logo

HAUSA

An samu karuwar matafiya a yayin hutun ranar ma’aikata a kasar Sin

2021-05-06 11:05:34 CRI

Ana sa ran jimilar tafiye-tafiyen fasinjoji da aka yi yayin hutun ranar ma’aikata a kasar Sin, zai kai miliyan 267, wanda ya nuna an samu karuwar adadi mai yawa na matafiya idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.

Ma’aikatar kula da sufuri ta kasar Sin ta ce, ana sa ran matsakaicin matakin tafiye-tafiye a kullum ya zarce miliyan 53.47, wanda zai karu da kaso 122.2 kan na bara.

Yayin da kasar Sin ta samu gagarumar nasara wajen kandagarki da dakile yaduwar COVID-19, Sinawa sun yi tururuwar tafiye-tafiye a lokacin hutun na kwanaki 5

Kusan tafiye-tafiye ta jiragen kasa miliyan 18.83 aka yi a ranar Asabar, wadda ita ce rana ta farko ta hutun, adadin da ya karu da kaso 9.2 akan na shekarar 2019, wanda kuma ya kai matsayin koli a rana 1.

A bangaren sufurin jiragen saman fasinja kuwa, tafiye tafiyen fasinjoji kusan miliyan 8.66 aka yi a lokacin hutun, wanda ya karu da kaso 173.9 akan na bara, dake mataki daya na shekarar 2019.

Hutun na ma’aikata kan fara ne daga ranar 1 zuwa 5 ga wata. (Fa’iza Mustapha)