logo

HAUSA

Kasuwar lantarki ta ECOWAS za ta share fagen bunkasa yankin in ji shugaban kungiyar

2021-05-06 09:59:16 CRI

Shugaban kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ECOWAS Jean-Claude Kassi Brou, ya bayyana kasuwar samar da lantarki ta yankin da ake ginawa, a matsayin matakin da zai habaka ci gaban kasashen yammacin Afirka.

Wata sanarwa da hukumar kungiyar ECOWAS mai lura da lantarki ko ERERA ta fitar a jiya Laraba, a madadin shugaban kungiyar, ta hakaito Brou na cewa, samar da lantarki zai zamo ginshikin wanzuwar kasuwar, kuma ECOWAS na tsara wasu manufofi, wadanda za su samar da kyakkyawan yanayi a fannin zuba jari, domin samar da makamashi.

Babban jami’in ya ce, burin shi ne jawo masu zuba jari zuwa ga fannin samar da lantarki, da fannonin rarrabawa da musayar shi tsakanin kasashe daban daban, ta yadda al’ummun shiyyar za su ci gajiya daga makamashin na lantarki bisa kariyar doka mafi dacewa.

Kaza lika Mr. Brou ya ce, matakan da kungiyar ECOWAS ke dauka, za su taimakawa sassa masu zaman kan su, sanin hakikanin dokokin zuba jari a sashen samar da lantarki ba tare da wata rufa rufa ba. (Saminu)