logo

HAUSA

Halayyar Amurka na boye alluran rigakafin COVID-19

2021-04-28 16:38:21 CRI

A yayin da wasu sassan duniya ke ci gaba da fama da annobar COVID-19, jama’a na bayyana bacin ransa a kafafen sada zumunta, game da hayayyar Amurka da ma kasashen yammacin duniya na boye alluran riga kafin COVID-19.

Halayyar Amurka na boye alluran rigakafin COVID-19_fororder_210505世界21016-hoto3

Wani rahoto da jaridar Times of India (TOI) ta wallafa, ya bayyana cewa, ana ta kara wallafa rahotannin kin jikin Amurka da na kasashen yamma a kafofin sada zumunta, tare da sukar gwamnatin Biden da Harris, kan yadda suka boye tarin alluran riga kafin ba tare da an fitar da su don a yiwa jama’a ba.

Rahoton ya kara da cewa, Amurka ta toshe kunnenta kan yadda cutar ke kara tsananta a kasashe kamar Indiya da Brazil, wadanda ke zama na daya da na biyu bi da bi da cutar ta fi kamari a duniya.

Cibiyar nan ta Duke ta kasa da kasa mai kula da harkar kiwon lafiya, ta ce jaridar TOI ta yi nuni da cewa, Amurka za ta kara samun alluran riga kafin fiye da kima har sama da miliyan 300 ko wasu karin riga kafin nan da watan Yuli, yayin da kasashe da dama sai sun jira shekaru, kafin su kammala yiwa riga kafin a kasashensu.

Halayyar Amurka na boye alluran rigakafin COVID-19_fororder_210505世界21016-hoto2

Wannan dabi’a a cewar rahoton, yana dakushe kokarin WHO na magance matsalar rashin daidaito wajen raba alluran riga kafin.

Wasu rahotanni na cewa, a kasar ta Indiya, kashi 1.4 bisa 100 na al’ummar kasar ne kadai suka samu cikakkun rigakafin, yayin da asibitocin kasar ke fama da karancin iskar oxygen. A kasar ta Amurka mutum guda cikin Amurkawa 4 ya samu cikakkun rigakafin, sannan sama da kashi 40 bisa 100 na ’yan kasar, sun karbi zagayen farko na rigakafin, asibitin Jackson Memorial dake Miami, ya bayyana cewa, zai fara dakatar da aikin rigakafin saboda alluran da ake samarwa na kara yin yawa, kana masu bukatar rigakafin na ci gaba da raguwa. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)