logo

HAUSA

An cimma nasarar gudanar da taron karawa juna sani mai taken "Sabon Tsarin JKS da sabuwar tafiyar Sin da Najeriya"

2021-04-24 17:14:33 cri

An cimma nasarar gudanar da taron karawa juna sani mai taken "Sabon Tsarin JKS da sabuwar tafiyar Sin da Najeriya"_fororder_微信图片_20210424170553

A gabannin cika shekaru 100 da kafuwar Jam'iyyar Kwaminis ta Sin, a yammacin ranar 22 ga watan Afrilu, an gudanar da taron karawa juna sani mai taken “Sabon Tsarin JKS da sabuwar tafiyar Sin da Najeriya” a cibiyar al'adun kasar Sin da ke Najeriya, wanda Ofishin Jakadancin kasar Sin da Ma'aikatar Watsa Labarai da Al'adu ta Najeriya suka dauki nauyin shiryawa, kana Cibiyar Al'adu ta kasar Sin da kungiyar daliban kasar Sin dake kasar, suka taimaka wajen shiryawa.

Jakadan kasar Sin dake Najeriya Cui Jianchun ya jaddada a cikin jawabinsa cewa, manufar Jam'iyyar Kwaminis ta Sin (JKS) ita ce dora muhimmanci kan jama'a da hidimta musu da zuciya daya. Ya ce a matsayinta na jam'iyya mai mulkin kasar Sin, yayin da take mai da hankali kan jin dadin rayuwar jama’ar kasar, tana kuma lura da yanayin duniya don neman raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga bil Adama.

Jakada Cui ya yi bayani kan tunaninsa game da bunkasa huldar dake tsakanin Sin da Najeriya, kuma ya jaddada cewa, a shirye take kasar Sin ta hada hannu da Najeriya don taka rawa mai armashi game da dangantakar dake tsakaninsu cikin shekaru 50 masu zuwa.

A nata jawabin, babbar sakatariyar ma'aikatar yada labarai da al'adu ta Najeriya Dr. Mrs. Ifeom. A. Anyanwutaku ta yaba sosai da manyan nasarorin da Sinawa suka samu karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a fannonin kyautata zaman rayuwar jama’a da bunkasa tattalin arziki da dai sauransu. Ta ce, an gudanar da wannan taron karawa juna sanin a lokacin da ya dace, wanda ya bayar da wani dandalin nuna dadaddiyar dangantakar abota dake tsakanin kasashen biyu. Ta ce barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a duniya, ta yi mummunan tasiri ga mu'amalar al'adu, amma ta yi imanin cewa, irin wannan taron zai taimaka wajen kyautata mu’amalar. (Bilkisu Xin)