logo

HAUSA

Hadarin jirgin kasa ya hallaka mutane 11 a Masar

2021-04-19 13:22:27 CRI

A kalla mutane 11 ne suka rasa rayukan su, kana wasu 98 suka jikkata, yayin da wani jirgin kasa ya zame daga layin dogo a jiya Lahadi, a birnin Toukh, dake arewa da birnin Alkahiran kasar Masar.

Wata sanarwa da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar, ta ce jim kadan da aukuwar al’amarin, an aike da motocin daukar marasa lafiya 60, domin kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti.

Sanarwar ta kara da cewa, jirgin kasan na dauke da tarago 4, a lokacin da ya zame daga kan layin dogon da yake kai. Tuni kuma shugaban kasar Abdel-Fattah al-Sisi, ya ba da umarnin kafa wani kwamiti, wanda zai gabatar da rahoto game da musabbabin aukuwar hadarin.

Ofishin mai gabatar da kara na kasar ya ce, za a bincike direban jirgin da mataimakin sa, da kuma karin wasu jami’ai 8 dake aiki a tashar jiragen kasa ta Toukh, domin tabbatar da dalilin aukuwar wannan ibtila’i.  (Saminu)