logo

HAUSA

Jakadan Sin ya bukaci a dauki kwararan matakan kawar da cin zarafi ta hanyar lalata

2021-04-15 10:04:26 CRI

Jakadan Sin ya bukaci a dauki kwararan matakan kawar da cin zarafi ta hanyar lalata_fororder_210415-MDD

A jiya Laraba wakilin kasar Sin a MDD ya bukaci kasa da kasa da su bullo da kwararan matakan yaki da cin zarafi ta hanyar lalata.

A yayin da ake tsaka da fuskantar annobar COVID-19, hare-haren kungiyoyin ’yan tada kayar baya da ayyukan ta’addanci ba su tsakaita ba, sannan yanayin bukatun jin kan dan Adam da matsalolin tsaro na ci gaba da tsananta. Cin zarafi ta hanyar lalata ana ci gaba da amfani da shi a matsayin yaki da kuma ta’addanci, mata dake fuskantar yake-yake sun fi shiga cikin mawuyacin hali, in ji Zhang Jun, zaunannen wakilin Sin a MDD.

Ya bayyanawa kwamitin sulhun MDD cewa, kasar Sin tana Allah wadai da yin amfani da cin zarafi ta hanyar lalata a matsayin yaki, kana tana Allah wadai da babbar murya game da dukkan nau’in cin zarafi ta hanyar lalata ga mata da kananan yara mata. Kasar Sin ta bukaci kasa da kasa da su dora muhimmanci kan wannan batu tare da aiwatar da kwararan matakan da za su kawar da dukkan nau’ikan cin zarafi masu alaka da yin lalata, kuma a yi kokarin daga darajar mata, da daga matsayin ajandar tabbatar da zaman lafiya da tsaro. (Ahmad)