logo

HAUSA

Rigakafin SINOVAC ya yi matukar tasiri a Turkiyya

2021-04-15 19:07:56 CRI

Rigakafin SINOVAC ya yi matukar tasiri a Turkiyya_fororder_疫苗-2

Wata majiyar watsa labarai ta kasar Japan, ta rawaito gwamnatin kasar Turkiyya na cewa, allurar rigakafin cutar COVID-19 na kamfanin SINOVAC na kasar Sin, ta yi matukar tasiri wajen dakile yaduwar cutar a Turkiyya.

An sanar da wannan sakamako ne, bayan nazartar yanayin lafiyar mutane miliyan 7.5 da aka yiwa rigakafin kamfanin na SINOVAC. A cewar ministan lafiyar Turkiyya, adadin masu harbuwa da COVID-19 ya ragu daga kaso 17.7% zuwa kaso 8.2%, tsakanin mutanen da shekarun su na haihuwa suka haura 65. (Saminu)