logo

HAUSA

Sin: Amincewar Amurka game da matakin Japan ba hujja ba ne

2021-04-15 19:04:43 CRI

Sin: Amincewar Amurka game da matakin Japan ba hujja ba ne_fororder_15

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce kasar sa da Koriya ta kudu, sun bayyana damuwa, da matukar rashin amincewa da matakin da gwamnatin Japan ta ce za ta dauka, na juye ruwan dagwalon nukiliyar cibiyarta ta Fukushima cikin teku.

Zhao Lijian ya yi wannan tsokaci ne a Alhamis din nan, lokacin da yake amsa tambaya da aka yi masa don gane da wannan batu, yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa.

Jami’in ya kuma yi kira ga Japan, da ta tattaunawa da hukumomin kasa da kasa, da ma kasashen dake makwaftaka da ita, ta yadda za a kai ga cimma matsaya karkashin shawarwarin dukkanin sassan masu ruwa da tsaki.

Ya ce ya kamata a yi matukar taka tsantsan, game da batun juye ruwan dagwalon cibiyar ta Fukushima cikin teku. Kuma bai kamata Japan ta dauki amincewar Amurka kan wannan batu a matsayin wani dalili, na samun nutsuwa game da matakin da take shirin aiwatarwa ba.

Da ya tabo batun kiran da ministan muhallin kasar Japan ya yiwa Sin kuwa, game da bukatar ta rage fitar da nau’o’in iska mai gurbata muhalli, Zhao Lijian ya ce har kullum, Sin a shirye take ta sauke nauyin dake wuyan ta yadda ya kamata, tana kuma shawartar Japan da ta warware na ta matsaloli da farko, ta kuma yi hangen nesa wajen warware batun ruwan dagwalon nukiliyar cibiyarta ta Fukushima.  (Saminu)