logo

HAUSA

Tsarin ilimin sana’o’i zai taimakawa raya masana’antun Sin da kasashen Afirka

2021-04-14 20:36:44 CRI

Tsarin ilimin sana’o’i zai taimakawa raya masana’antun Sin da kasashen Afirka_fororder_ilimi-0

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a kara azama, wajen gaggauta gina tsarin ilimin sana’o’i na zamani, tare da samar da karin kwarewa a wannan fanni. Inda ya ce tsarin ba da ilimin sana’o’i na da matukar muhimmanci, domin ta wannan bangare ne ake samar da dimbin kwararrun ma’aikata da ake bukata, wadanda suke ba da taimako ga aikin raya masana’antu.

Shugaba Xi ya bayyana hakan ne a kwanakin baya, cikin wani umarni da ya bayar, don gane da burin kasar Sin na bunkasa ilimin koyar da sana’o’i. Ya ce akwai bukatar gudanar da sauye sauye a fannin horaswa, da mayar da tsarin bisa salo na makarantu, tare da kyautata salon gudanarwa, da tallafi da ake baiwa bangaren.

Ya kuma yi kira da a daga matsayin sashen, ta yadda za a rika bayar da digiri a fannin koyon sana’o’i, tare da kara adadin kwalejoji, da cibiyoyin dake ba da horo a sassan ilimin sana’o’in.

Daga nan sai ya yi kira ga hukumomin gwamnati a dukkanin matakai, da su kirkiro sabbin cibiyoyi, da kyautata dabarun tallafawa, da zuba jari, ta yadda za a kara bunkasa sana’o’in hannu, da daga darajar kwararrun dake ba da gudummawa a fannin raya su.

Tsarin ilimin sana’o’i zai taimakawa raya masana’antun Sin da kasashen Afirka_fororder_ilimi-1

Yanzu haka an riga an kafa wani tsarin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, inda ake gayyatar dalibai ‘yan Afirka, don su zo kasar Sin domin koyon ilimin sana’o’i daban daban, kana ana tura kwararru zuwa wasu kasashen Afirka, irinsu Sudan, da Burkina Faso da dai sauransu, domin taimakawa wajen gina tsarin ilimin sana’o’i a can. Ta wannan tsari na hadin gwiwa, ake sa ran ganin an samar da karin kwararrun ma’aikata a kasashen Afirka, wadanda za su taka muhimmiyar rawa, a kokarin raya masana’antun kasashensu. (Bello Wang)

Bello