logo

HAUSA

Sabon jakadan Sin a Najeriya ya gana da ministan harkokin wajen kasar

2021-04-14 21:11:51 CRI

Sabon jakadan Sin a Najeriya ya gana da ministan harkokin wajen kasar_fororder_3

A jiya Talata ne sabon jakadan Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya kaiwa ministan harkokin wajen Najeriya Godfrey Onyeama ziyara a ofishin sa.

Yayin da suke zantawa da juna, jakada Cui ya ce yana alfahari da kasancewa jakadan Sin a Najeriya. Ya ce cikin shekaru sama da 50, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Najeriya, huldar musamman tsakanin kasashen biyu na kara fadada sannu a hankali.

Jakadan ya kara da cewa, Sin a shirye take ta yi aiki tare da Najeriya, a fannin tsara hadin gwiwar samar da ababen more rayuwa, da bunkasa fannin sadarwa, da raya masana’antu, da zuba jari da cinikayya, ta yadda hakan zai bunkasa moriyar kasashen biyu, da kuma al’ummun su.

Shi kuwa a nasa bangare, Mr. Onyeama maraba ya yi da zuwan jakada Cui, yana mai cewa, Sin da Najeriya sun shafe tsawon shekaru suna kyautata kawance. Kaza lika a tsawon lokacin, Sin ta sha taimakawa Najeriya a fannin ginin hanyoyi, da layin dogo, da tashoshin ruwa, da na samar da lantarki da sauran su. Ta kuma baiwa Najeriya babbar gudummawa, wajen inganta samar da ababen more rayuwa. Don haka Najeriya na matukar godiya ga kasar Sin. (Saminu)