logo

HAUSA

Mauritius ta karbi kashin farko na riga-kafin COVID-19 daga kasar Sin

2021-04-14 14:17:40 CRI

Mauritius ta karbi kashin farko na riga-kafin COVID-19 daga kasar Sin_fororder_210414-Mauritius

Da yammacin ranar Talata kashin farko na alluran riga-kafin COVID-19 na kamfanin Sinopharm na kasar Sin ya isa kasar Mauritius domin tallafawa kasar aikin riga-kafin yaki da annobar ta COVID-19.

Ministan harkokin wajen kasar Mauritius Alan Ganoo, da ministan lafiyar kasar Kailesh Jagutpal, da jami’in harkokin diflomasiyyar kasar Sin a kasar Mauritius Gong Yufeng, sun halarci bikin mika gudunmawar a filin jirgin sama na kasa da kasa na Sir Seewoosagur Ramgoolam.

A jawabin da ya gabatar a lokacin bikin, Ganoo ya yi maraba da zuwan riga-kafin na kasar Sin. Ya bayyana cewa, kasar Mauritius tana matukar nuna godiya ga gwamnatin Sin saboda samarwa kasar riga-kafin a daidai lokacin da ake fuskantar wahalhalu, wanda hakan yana kara nuna matsayin dangantaka da aminantaka a tsakanin kasashen Mauritius da Sin. (Ahmad)