logo

HAUSA

‘Yan bindiga sun halaka mutane biyar a yankin arewa maso yammacin Najeriya

2021-04-13 12:55:24 CRI

Rahotanni daga Najeriya na cewa, wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kashe mutane biyar, bayan da suka yiwa kauyen Wawa Rafi II dake karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna dake yankin arewa maso yammacin kasar kawanya.

Da yake Karin haske cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar ta Kaduna Samuel Aruwan, ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kuma kai hari karamar hukumar Giwa dake jihar ta Kaduna.

Aruwan ya bayyana cewa, an kashe wani magidanci da kuma dansa mai shekara 7, a harin da ‘yan bindigar suka kai, baya ga wasu karin gawarwaki biyu da jami’an tsaro suka gano daga bisani. A wani hari na daban kuma, ‘yan bindigar sun farma wata gonar rake, inda suka harbe wani mazaunin kauyen har lahira.

Yankin arewacin kasar ta Najeriya dai, ya sha fama da jerin hare-haren ‘yan bindiga, wadanda suka haddasa mutuwar fararen hula da ma hasarar dukiyoyi.(Ibrahim)