Yawan bukatun mallakar fasahar AI na kasar Sin cikin shekaru 10 da suka gabata ya kai matsayi na farko a duniya
2021-04-13 10:48:02 CRI
Bisa rahoton bunkasuwar kwaikwayon fasahar tunanin dan Adam wato AI na kasar Sin na shekarar 2020 da aka gabatar a kwanakin baya, an ce, a cikin shekaru 10 da suka gabata, yawan bukatar mallakar fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam na duniya ya zarce dubu 520, daga cikin adadin yawan na kasar Sin ya kai 389,571, wanda ya kai kashi 74.7 cikin dari inda ya kai matsayin farko a duniya.
Haka zalika, yawan na’urorin sarrafa harsuna, da fasahar kananan na’urorin lantarki, da sauransu a fannin fasahar AI ya kai matsayin gaba a duniya.
Rahoton ya yi bincike kan albarkatun kwararru a fannin fasahar AI a duniya, ya yi nuni da cewa, yawan kwararrun ya fi yawa a kasar Amurka, yawansu ya kai 1244, kuma kasar Sin ta zama matsayi na biyu a wannan fanni, yawansu ya kai 196, wadanda suka zauna a yankunan Beijing, da Tianjin, da lardin Hebei, da yankin kogin Yangtze Delta, da kuma yankin kogin Zhujiang Delta. (Zainab)