logo

HAUSA

Brazil ta gabatar da sakamakon gwajin alluran rigakafin COVID-19 na kamfanin Sinovac a mataki na uku

2021-04-12 16:08:52 CRI

Brazil ta gabatar da sakamakon gwajin alluran rigakafin COVID-19 na kamfanin Sinovac a mataki na uku_fororder_hoto2

Jiya Lahadi, cibiyar nazari ta Butantan ta jihar Sao Paulo dake kasar Brazil, ta gabatar da sakamakon mataki na uku na gwajin alluran rigakafin COVID-19 na CoronaVac, na kamfanin Sinovac na kasar Sin, inda ta daga matsayin amfanin alluran rigakafin CoronaVac kan wadanda suka kamu da cutar COVID-19, amma babu bukatar ganin likita, daga 50.38% a watan Janairu zuwa 50.7%, kuma, ta daga amfanin alluran rigakafin CoronaVac kan wadanda suka kamu da cutar, wadanda ke bukatar ganin likita, daga 78% a watan Janairu zuwa 83.7%.

Binciken cibiyar ya nuna cewa, alluran rigakafin CoronaVac suna iya ba da kariya ga sabbin kwayoyin cutar COVID-19, wato P.1 da kuma P.2. An gano sabuwar kwayar cutar P.1 a birnin Manaus na jihar Amazonas ta kasar Brazil, wadda ta haddasa sake barkewar cutar numfashi ta COVID-19 a kasar Brazil. Kuma, an gano sabuwar kwayar cutar P.2 a birnin Rio de Janeiro da wasu sassan kasar. (Maryam)