logo

HAUSA

Jam'iyyar ACP ta Australia ta tona asirin wasu kasashen yamma game da amfani da yankin Xinjiang don haifar da matsala ga Sin

2021-04-12 20:58:43 CRI

Jami’yyar ACP ta Australia ta tona asirin wasu kasashen yamma game da amfani da yankin Xinjiang don haifar da matsala ga Sin_fororder_3

A farkon watan nan na Afirilu ne jamiyyar ACP ta Australia, ta wallafa wani rahoton musamman, mai taken “Xinjiang: kan iyakar Sin ta yamma, zuciyar Turai da Asiya”, inda a cikin sa ta fallasa mummunar aniyar wasu kasashen yammacin duniya irin su Amurka da Birtaniya, don gane da shirin su na mara baya ga ‘yan aware, da masu ayyukan ta’addanci, don cimma wasu manufofin siyasa, tare da fatan haifar da matsala ga kasar Sin, ta yadda za su dakushe ci gaban kasar.

Rahoton ya yi bayani dalla dalla cikin babuka 8, inda ya yi nuni da yadda bisa tarihi, manufofin kasashe irin su Amurka, da Birtaniya, da Turai da wasu sassan Asiya, suka haifar da rashin zaman lafiya a wannan yanki.

Har ila yau, rahoton ya ce tun a wajen shekarar 2003, hukumar leken asiri ta CIA, ta gabatar da shawarar dake nuna yiwuwar Amurka ta yi amfani da batun Xinjiang, don yiwa kasar Sin matsin lamba, a duk lokacin da take da wani takun saka da Sin.

Bisa wannan dalili ne kuma, Birtaniya, da Amurka da kawayen su, suke amfani da wasu kungiyoyi na ‘yan kabilar Uyghur dake zaune a kasashen ketare, suna kitsa karairayi game da Xinjiang, tare da tsara amfani da kafafen watsa labarai na yammacin duniya, don yada wadannan farfaganda.

Kaza lika rohoton ya kara da fallasa shirin Amurka da Birtaniya, na daukar nauyin ayyukan ‘yan aware, da karfafa gwiwar masu ayyukan ta’addanci, don cimma bukatar ci gaba da yin babakere, da tabbatar da mulkin mulaka’u.

A wani bangaren kuma, rahoton wanda jam’iyyar ta ACP ta wallafa a shafin ta na yanar gizo, ya ce ko shakka babu, a baya bayan nan, kasar Sin ta zama wani muhimmin karfi na bunkasa tattalin arzikin duniya, kuma rashin hankali ne wasu kasashe ko sassa, su yi amfani da batun da ya shafi Xinjiang wajen muzgunawa kasar Sin. (Saminu)