logo

HAUSA

An fara zaben shugaban kasa a kasar Benin

2021-04-12 09:58:37 CRI

An fara zaben shugaban kasa a kasar Benin_fororder_210412-Benin

An fara kada kuri’a a zagayen farko na zaben shugaban kasa jiya Lahadi a kasar Benin, a galibin tashoshin zabe dake sassa daban-daban na kasar.

Kimanin masu zabe miliyan 5 ne ake sa ran za su kada kuri’unsu, a rumfunan zabe 15,531 dake sassan kasar da kuma wasu tashohin zabe 11 da aka tanada a wasu kasashen ketare 7 a zagayen farko na zaben.

Bisa sabuwar dokar zabe ta kasar, za a zabi shugaban kasa da mataimaikinsa ta hanyar baiwa wadanda suka cancanci zabe damar kada kuri’unsu, bisa wa’adin shekaru biyar, za kuma a sake zabensa sau daya tak.

Yanzu haka dai, ’yan takara uku ne suke fafatawa a wannan zabe. Shugaba mai ci Patrice Talon da mataimakiyarsa Mariam Talata, za su fuskanci adawa daga Corentin Kohoue-Irene Agossa na jam’iyyar RLC da Alassane Soumanou-Paul Hounkpe na jam’iyyar FCBE.

Da yake jawabi bayan kada kuri’arsa a birnin Cotonou, cibiyar kasuwancin kasar, shugaba Talon ya yi kira ga ’yan kasar, da su fito kwansu da kwarkwata, domin sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ba su na yin zabe. Yana mai cewa, zaben na gudana a sassan kasar ba tare da wata matsala ba. (Ibrahim)