logo

HAUSA

Somaliya ta karbi tallafin alluran riga kafin Sinopharm da kasar Sin ta baiwa kasar

2021-04-12 09:37:48 CRI

Somaliya ta karbi tallafin alluran riga kafin Sinopharm da kasar Sin ta baiwa kasar_fororder_210412-Somalia

A jiya ne kasar Somaliya, ta karbi tallafin alluran riga kafin kamfanin Sinopharm 200,000 da kasar Sin ta baiwa kasar, domin taimakawa yakin da kasar dake kahon Afirka ke yi da annobar COVID-19.

A jawabinta bayan karbar tallafin riga kafin, ministar lafiya da hidimomin jama’a ta Somaliya Fawziya Abikar Nur, ta yaba taimakon da kasar Sin ta baiwa kasarta, a wani muhimmin lokaci da take yaki da annobar COVID-19. Tana mai cewa, mutane 100,000 ake sa ran za su amfana da riga kafin.

Ta bayyana cewa, “yau mun karbi tallafin alluran rigan kafi na kamfanin Sinopharm na kasar Sin guda 200,000. Za kuma su taimaka mana a yakin da muke yi da wannan annoba. A don haka, muna godiya ga kasar Sin bisa boyon bayan da take baiwa gwamnati da al’ummar kasar Somaliya. Tana mai cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana tare da Somaliya baya ga taimakon da take ba ta.”

A nasa jawabin jakadan Sin dake Somaliya Qin Jian, ya bayyana cewa, kasar Sin ce kasa ta farko da ta taimakawa Somaliya da alluran riga kafi, za kuma ta ci gaba da taimakawa Somaliya a wani mataki na bunkasa alakar dake tsakanin kasashen biyu.

Qin ya bayyana cewa, kasar Sin ta cika alkawarinta, na ganin alluran riga kafin COVID-19 sun zama hajar al’ummar duniya kamar yadda hakan ya tabbata a zahiri, da yayata raba riga kafin ga kasashen duniya bisa adalci, da tabbatar da gudummawar kasar Sin na ganin kasashe masu tasowa sun samu alluran riga kafin cikin sauki da kuma araha. (Ibrahim)