logo

HAUSA

An kaddamar da zaben shugaban kasar Chadi

2021-04-12 10:09:11 CRI

An kaddamar da zaben shugaban kasar Chadi_fororder_1

An kaddamar da zaben shugaban kasa a Chadi a jiya Lahadi, inda jama’ar kasar ta tsakiyar Afirka suka fita don kada kuri’a.

‘Yan takara 7, ciki har da shugaba mai ci Idriss Derby Itno ne, ke neman kujerar shugabancin kasar na tsawon wa’adin shekaru 6 masu zuwa. Tsohon firaministan kasar, Pahimi Padacket Albert ne babban abokin hamayyar shugaban mai ci a zaben.

Yayin gangamin yakin neman zabensa na karshe, wanda ya gudana ranar Jumma’a a babban birnin N’Djamena, shugaba Deby ya yi kira ga magoya bayansa da su fita su kada kuri’a, yana mai tabbatar musu cewa shi zai lashe zaben.

A farkon watan Maris ne ‘yan takara 3 na bangaren adawa suka janye daga shiga zaben, cikinsu har da babban dan adawa Saleh Kebzabo, wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasar da aka yi a shekarar 2016.

Sama da mutane miliyan 7.3 ne suka cancanci kada kuri’a a wannan karon, kamar yadda hukumar zaben kasar mai zaman kanta CENI, ta bayyana.

A cewar hukumar, za a sanar da kwarya-kwaryar sakamakon zaben ne a cikin makonni biyu masu zuwa. (Fa’iza Mustapha)