logo

HAUSA

Kasar Sin za ta shirya shagulgula da dama yayin bikin cika shekaru 100 da kafuwar JKS

2021-04-12 10:19:57 CRI

Kasar Sin za ta shirya shagulgula da dama yayin bikin cika shekaru 100 da kafuwar JKS_fororder_210412-CPC

Rahotanni daga kasar Sin na cewa, za a shirya kasaitattun shagulgula, yayin bikin cika shekaru 100 da kafuwar JKS.

Wata sanarwa da babban ofishin kwamitin koli na JKS ya fitar, ta nuna cewa, za a shirya shagulgula daban-daban, don fito da rawar da jam’iyyar ta taka, yayin da sojojin kasar gami da daukin al’ummar Sinawa daga kungiyoyin kananan kabilu, za su nace ga burin da ake fatan cimmawa, da nacewa kan wannan buri, da yin aiki tukuru wajen ganin sun bayar da gudummawarsu.

Sanarwar ta kuma yi kira da a shirye wadannan shagulgula ta hanyar kirkire-kirkire da matakan da suka shafi jama’a, ta yadda za su yi tasiri da kuma kayatarwa. (Ibrahim Yaya)