logo

HAUSA

Shugaban Comoros ya karbi allurar rigakafin Sin

2021-04-11 16:22:47 CRI

Shugaban Comoros ya karbi allurar rigakafin Sin_fororder_2

Rahotanni sun nuna cewa, an kaddamar da aikin yi wa al’ummun kasar Comoros allurar rigakafin cutar COVID-19 a Moroni, babban birnin kasar a hukumance a jiya, inda aka yi wa shugaban kasar Azali Assoumani, allurar ta farko ta kamfanin Sinopharm na kasar Sin.

Jakadan kasar Sin dake kasar ta Comoros He Yanjun, da likitocin da kasar Sin ta tura zuwa kasar da wasu jami’an gwamnatin Coromos sama da goma sun halarci bikin da aka shirya, inda shugaba Azali ya nuwa godiya ga kasar Sin saboda tallafin allurar rigakafin da ta samar wa kasarsa, kuma ya yi nuni da cewa, kaddamar da aikin yin allurar ya alamta cewa, aikin kandagarkin annobar a Comoros ya shiga wani sabon mataki.

Shugaban Comoros ya karbi allurar rigakafin Sin_fororder_1

A nasa bangaren, jakadan kasar Sin He Yanjun, ya gabatar da jawabi yayin bikin, inda ya bayyana cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana maida hankali matuka kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, kuma tana fatan kasashe wadanda suke da karfin taimakawa saura su samar da tallafi ga kasashe masu bukata tun da wur wuri, musamman ma ga kasashe masu tasowa wadanda ke bukatar tallafin, ta yadda al’ummomin kasashen duniya za su ci gajiya daga allurar.

Bisa bukatar gwamnatin kasar Comoros, tawagar ma’aikatan lafiya ta kasar Sin ta isa Moroni, a ranar 17 ga watan Maris, tare da allurar rigakafin da kayayyakin kiwon lafiya.(Jamila)