logo

HAUSA

Ikenna Emewu: Kasar Amurka tana da mugun manufar dakatar da ci gaban kasar Sin

2021-04-09 11:39:13 CRI

Ikenna Emewu: Kasar Amurka tana da mugun manufar dakatar da ci gaban kasar Sin_fororder_微信截图_20210409112108

A ran 6 ga watan, jaridar “The Authority Daily” ta kasar Najeriya ta wallafa wani bayani mai taken ‘Shirin bidiyon da aka tona ya bayyana yadda kasar Amurka take yunkurin dakatar da ci gaban kasar Sin bisa hujjar hakkin dan Adam na Xinjiang” da malam Ikenna Emewu, shugaban cibiyar kafofin yada labaru na kasashen Afirka da Sin ta Najeriya ya rubuta. A cikin bayaninsa, malam Ikenna Emewu ya nuna cewa, yanzu kasar Amurka da wasu kasashen yammacin duniya suna ta yada jita-jita game da hakkin dan Adam na Xinjiang na kasar Sin, har ma sun ba aikin “bata sunan kasar Sin” muhimmanci fiye da komai. Amma a cikin wani shirin bidiyo da aka tona a kwanan baya, Lawrence Wilkerson, direktan ofishin kula da harkokin Colin Luther Powell, tsohon sakataren kula da harkokin wajen kasar Amurka, ya tona asiri cewa, dalilin da ya sa kasar Amurka ta jibge sojojinta a kasar Afghanistan, shi ne, tana son “dakatar da ci gaban kasar Sin” da “ta da zaune tsaye a kasar Sin”, sannan “yin amfani da ’yan kabilar Uygur don su murkushe kasar Sin kai tsaye”. Lalle, jawabin Lawrence Wilkerson ya tona hakikanin dalilin da ya sa kasar Amurka ta yi ta yada jita-jita game da jihar Xinjiang ta kasar Sin.

A cikin bayaninsa, malam Ikenna Emewu ya kara da cewa, “dakatar da ci gaban kasar Sin”, har ma “kasar Sin ta ba da kai a gaban kasar Amurka”, sun riga sun zama babban burin da gwamnatin kasar Amurka take son cimmawa. Gwamnatin Joe Biden ta ci gaba da aiwatar da manufar nuna adawa da kasar Sin da gwamnatin Donald Trump ta tsara, musamman a fannin amfani da wai batun hakkin dan Adam na Xinjiang. Bayan sabuwar gwamnatin Amurka ta gyara huldar dake tsakaninta da kasashen Turai, kasashe kawayenta na Turai sun kuma shiga wannan muhawara da kasar Sin. Wannan shirin bidiyon da aka ambata a baya, ya bayyana cewa, ko ana kokarin boye shi, “tabbas hakikanin abubuwa su kan fito lokaci lokaci daga aljihun da aka rufe su.” Da farko dai, yin amfani da wai batun hakkin dan Adam na Xinjiang, wani kwaikwayo ne da bangaren Amurka ya mai da hankali sosai wajen zana shi domin kai hari kan kasar Sin. Dalilin da ya sa ya yi haka shi ne, Amurka ba ta son kasar Sin ta samu ci gaba balle ta zama wata kasa mai karfi sosai.

Sannan a cikin bayaninsa, malam Ikenna Emewu ya ce, wasu kungiyoyin ta’addanci, musamman kungiyar “East Turkestan Islamic Movement” ta kan kai hare-hare irin na ta’addanci a yankin Xinjiang a tsakanin shekarar 1992 da ta 2014, inda aka hallaka mutane masu dimbin yawa, tare da asarar dukiyoyi da yawa. Sabo da haka, gwamnatin kasar Sin ta dauki dimbin matakai domin tabbatar da kwanciyar hankali a jihar Xinjiang. Wadannan matakai sun kuma bayar da gudummawa sosai. Amurka na zarge-zarge ne kan kasar Sin ba gaira ba dalili. Bugu da kari, a lokacin da ake jin zarge-zargen da kasar Amurka da sauran kasashen yammacin duniya suka yi wa kasar Sin bisa hujjar hakkin dan Adam, mu kan tuna da zarge-zargen da wasu kungiyoyin hakkin dan Adam na kasa da kasa suka yi wa matakan dakile kungiyar “Boko Haram” da rundunar sojin Najeriya ta dauka. Ko Amurkawa sun fi mai da hankali wajen kare hakkin ’yan ta’adda? (Sanusi Chen)