logo

HAUSA

Sama da Amurkawa 20,000 sun harbu da sabbin nau’ikan cutar COVID-19

2021-04-09 17:23:28 CRI

Sama da Amurkawa 20,000 sun harbu da sabbin nau’ikan cutar COVID-19_fororder_20210409美国新冠

Cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta Amurka ko CDC, ta ce ya zuwa jiya Alhamis, sama da ’yan kasar 20,000 ne aka tabbatar sun harbu da sabbin nau’ikan cutar numfashi ta COVID-19.

Alkaluman cibiyar sun nuna cewa, duk da gaggauta yawan rigakafin da ake yiwa ’yan kasar, sabbin nau’ikan cutar na kara bazuwa cikin sauri, yayin da kwararru ke kashedin cewa, wadannan sabbin nau’ikan COVID-19 na iya dakile saurin farfadowar kasar daga wannan annoba.

Ya zuwa jiya Alhamis, an yiwa Amurkawa miliyan 174 rigakafin cutar ta COVID-19, yayin da kuma aka raba sama da alluran rigakafin cutar miliyan 229 zuwa sassan kasar daban daban.

A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban Amurka Joe Biden, ya sanar da cewa, ya zuwa ranar 19 ga watan Afirilun nan, daukacin Amurkawa baligai, za su samu damar yin rigakafin COVID-19, ko da yake dai a baya, an dage wa’adin farko na cimma wannan mataki da kusan makwanni 2. (Saminu)