logo

HAUSA

Tashar samar da lantarki daga hasken rana da Sin ta bada kudin kafawa ya samar da wutar lantarki ga asibitin yara a Gaza

2021-04-08 09:48:26 CRI

Tashar samar da lantarki daga hasken rana da Sin ta bada kudin kafawa ya samar da wutar lantarki ga asibitin yara a Gaza_fororder_210408-Palesdinu

Yankin Zirin Gaza da dakaru suka yi wa kawanya, ya kaddamar da tashar wutar lantarki daga hasken rana da kasar Sin ta samar da kudin kafawa, inda tashar ta samar da wuta ga wani asibitin yara.

An aiwatar da aikin kafa tashar lantarki daga hasken rana wadda za ta iya samar da lantarki mai karfin KW 30 ga asibitin yara na Al-Durrah dake birnin Gaza ne ta hannun wata kungiyar agaji ta Falasdinawa.

Yayin wani bikin da aka yi ta intanet, Guo Wei, shugaban ofishin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin dake Falasdinu, ya ce kasar Sin na da niyyar aiwatar da ayyukan da za su taimaka wajen inganta rayuwar Falasdinawa bisa bukatunsu, tare da samar musu karin abubuwan da za su ci gajiya.

A nasa bangaren, sakataren kungiyar agajin, Emad al-Agha cewa ya yi, tashar wadda kasar Sin ta samar da kudin aiwatar da ita, za ta samar da kaso 60 na wutan da ake bukata wajen tafiyar da asibitin yara na Al-Durrah.

Ya kara da cewa, taimakon da Sin ta ba asibitin, ci gaba ne kan irin abubuwan da Sin din ke samarwa Falasdinawa a dukkan matakai, musamman a bangaren bukatun yara. (Fa’iza Mustapha)