logo

HAUSA

WHO: Mai yiwuwa ne rigakafin COVID-19 na AstraZeneca yana daskarar da jini amma ba a tabbatar da hakan ba

2021-04-08 09:53:24 CRI

WHO: Mai yiwuwa ne rigakafin COVID-19 na AstraZeneca yana daskarar da jini amma ba a tabbatar da hakan ba_fororder_2

Ana tsammanin alluran rigakafin COVID-19 na kamfanin AstraZeneca yana haifar da daskarewar jini da kuma karancin motsawar jinin a jikin bil adama, sai dai hukumar lafiya ta duniya WHO ba ta tabbatar da hakan ba.

Tun da farko, hukumar kula da lafiya ta kasashen Turai (EMA) ta tabbatar cewa, an samu rahoton daskarewar jini da karancin motsawar jinin dake da alaka da amfani da rigakafin COVID-19 na kamfanin AstraZeneca, sai dai duk da hakan an bayyana hakan a matsayin mafi karancin tasiri na sauyin da allurar rigakafin ke haifarwa ga jikin dan adam.

A wata kwarya-kwaryar sanarwa, kwamitin ba da shawara kan ingancin alluran rigakafi na kasa da kasa na hukumar WHO (GACVS), ya bayyana cewa, al’amurran da ake tantancewar ba su da wani girma sosai, kuma babu wani adadi mai yawa da aka samu na rahotannin binciken da aka gudanar kan mutane miliyan 200 a duniya da aka yiwa rigakafin na AstraZeneca.

Sai dai kuma, akwai bukatar a gudanar da bincike na musamman domin a samu cikakkiyar fahimta game da al’amurran da ake zargin, kana kwamitin GACVS ya ba da tabbacin ci gaba da tattara alkaluma da kuma yin nazari kan su.(Ahmad)