logo

HAUSA

Shugaban Rwanda ya koka game da yadda wasu kasashe suka ki amincewa da hukunta masu hannu a kisan kiyashi

2021-04-08 09:39:45 CRI

Shugaban Rwanda ya koka game da yadda wasu kasashe suka ki amincewa da hukunta masu hannu a kisan kiyashi_fororder_11

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, ya koka game da yadda wasu kasashe ciki har da Faransa, suka ki amincewa su mikawa Rwandan mutanen da ake zargi da hannu, a kisan kiyashin kasar da ya auku cikin shekarar 1994.

Shugaba Kagame wanda ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin bikin cika shekaru 27 da kisan kiyashin da aka yiwa ‘yan kabilar Tutsi a Rwanda, ya ce masu hannu a aikata wannan ta’asa, na samun mafaka a kasashe da dama ciki har da Faransa, yayin da irin wadancan kasashe ke ci gaba da yin watsi da kiraye kirayen da Rwanda ke yi, na a mika su domin su fuskanci hukunci.

Ya ce yanzu haka akwai wasu shari’u masu alaka da hakan, da aka shafe tsawon kusan shekaru 15 ana yin su a Turai, da wasu kasashen Afirka, ba tare da an kai ga yanke hukunci ba.

Kaza lika akwai kasashen da ke rike da wadanda ake zargi mutane 4 ko 5, wadanda aka tattara cikakkun shaidu a kan su, amma an yi watsi da bukatar Rwanda ta mayar da su kasar su fuskanci hukunci. 

Rwanda wanda ke yankin tsakiyar Afirka, ta fara tarukan nuna alhinin kisan kiyashin da ya rutsa da sama da ‘yan kasar miliyan 1, yayin tashe tashen hankula na tsawon watanni 3.

Sama da ‘yan kasar 500, da baki aminanta, da wakilan ofisoshin jakadancin kasashen waje dake kasar ne suka halarci taron da gwamnatin kasar ta shirya, a rufaffen filin wasa na Kigali Arena, wanda ke birnin Kigali, ko da yake a bana, ba a gayyaci mutane da dama halartar taron ba, saboda kaucewa bazuwar cutar COVID-19.  (Saminu)