logo

HAUSA

Gwamnatin Zimbabwe ta sha alwashin wadata kasa da abinci nan da shekarar 2022

2021-04-08 10:03:13 CRI

Gwamnatin Zimbabwe ta sha alwashin wadata kasa da abinci nan da shekarar 2022_fororder_丰收

Ministan ma’aikatar noma a Zimbabwe Anxious Masuka, ya ce kasar sa na da shirin tabbatar da samar da isasshen abinci da al’ummar kasar ke bukata nan da shekarar 2022 dake tafe, tare da fadada kudaden shigar al’ummar ta da kaso 100 zuwa shekarar 2024.

Minista Masuka, ya ce baya ga burin kasar na dakatar da sayo abinci daga ketare, wanda hakan ke haifar da asarar kudaden fito, gwamnatin Zimbabwe na kuma fatan daga darajar albarkatun gona da kasar ke samarwa da kaso 40 bisa dari, ta yadda hakan zai samar da karin guraben ayyukan yi kimanin miliyan 1 ga ‘yan kasar, tare da kara yawan albarkatun gona da kasar ke fitarwa ketare da kaso 60 bisa dari nan da shekarar 2024.

Bugu da kari, gwamnati na hankoron sauya yadda kananan manoma kusan 18,000 ke gudanar da sana’ar su, zuwa kamfanonin aikin noma nan da shekarar 2025.

Zimbabwe na fatan cimma wadannan nasarori ne, bayan da ta kaddamar da shirin sauya tsarin noma a kasar mai lakabin AFTSTS a shekarar bara, da nufin gaggauta samar da albarkatun noma, da inganta su, da bunkasa sana’ar baki daya.  (Saminu)