logo

HAUSA

Amurka: Kasar ba ta canja shirinta na halartar gasar Olympic na birnin Beijing

2021-04-08 10:24:59 CRI

Jiya Laraba, kakakin fadar White House Jennifer Psaki ta nuna cewa, kasar ba ta canja shirinta na halartar gasar Olympic ta lokacin hunturu da za a yi a birnin Beijing a shekarar 2022 ba.

Kafin wannan kuma, maganar da kakakin majalisar gudanarwar kasar Amurka Ned Price ya yi a gun taron manema labarai da aka yi a ran 6 ga watan ta jawo hankalin kafofin yada labarai da dama, har an ruwaito cewa, wannan magana na nuna cewa, Amurka da kawayenta na yin la’akarin kin halartar gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing. (Amina Xu)