logo

HAUSA

Najeriya: Dalibai 5 da aka yi garkuwa da su sun kubuta

2021-04-07 09:38:44 CRI

Najeriya: Dalibai 5 da aka yi garkuwa da su sun kubuta_fororder_kaduna

Dalibai 5 ciki 39 ‘yan makarantar koyon ilimin gandun daji dake jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya, da wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da su tun cikin watan Maris da ya gabata sun kubuta.

Wata sanarwar da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ta Kaduna Samuel Aruwan ya fitar, ta bayyana cewa, rundunar sojojin kasar ta sanar da gwamnatin jihar cewa, daliban su 5 na samun kulawar lafiya, a wani wuri dake karkashin ikon rundunar.

A ranar 11 ga watan Maris da ya gabata ne dai wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, suka yi garkuwa da dalibai 39 daga kwalejin ta tarayya dake yankin Afaka na karamar hukumar Igabin jihar Kaduna.  (Saminu)

Bello