logo

HAUSA

IMF ya daga hasashen saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya a sakamakon hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa

2021-04-07 21:23:32 CRI

Game da sabon rahoton da asusun IMF ya fitar game da kara hasashen da ya yi kan saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau cewa, asusun IMF ya yi hasashen cewa tattalin arzikin duniya zai kara farfadowa, za kuma a samu wannan sakamako ne, idan kasa da kasa sun yi hadin gwiwa a tsakaninsu wajen yaki da cutar COVID-19, da sa kaimi ga farfado da masana’antu, wannan ya shaida amfani da wajibcin kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa don tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta. (Zainab)