logo

HAUSA

Kotun tsarin mulkin Kongo ta tabbatar da sake zabar shugaban kasar Denis Sassou Nguesso

2021-04-07 14:40:55 CRI

Kotun tsarin mulkin Kongo ta tabbatar da sake zabar shugaban kasar Denis Sassou Nguesso_fororder_210407-Kongo Bra

A jiya Talata kotun tsarin mulkin kasar Kongo ta tabbatar da sake zabar shugaban kasar mai ci Denis Sassou Nguesso bayan da kwarya-kwaryar sakamakon zaben ya tabbatar da nasarar shugaban kasar dake tsakiyar nahiyar Afrika makonni biyun da suka gabata.

Sassou Nguesso ya lashe kashi 88.4 bisa 100 inda ya yi nasara a kan abokin hamayyarsa Guy Brice Parfait Kolelas wanda ya samu kashi 7.96 bisa 100, sai kuma Mathias Dzon, mai kashi 1.92 bisa 100, a cewar kotun.

Baki daya, zaben kasar ya gudana ne salin alin ba tare da wata tangarda ba, kamar yadda ministan cikin gidan kasar Raymond Mboulou ya bayyana a jawabinsa ta gidan talabijin din kasar.

A cikin rahotannin da suka bayar a ranar 23 ga watan Maris game da zaben shugaban kasar na ranar 21 ga watan Maris, tawagogin masu sa ido a zaben da dama, musamman kungiyar hadin gwiwar kasashen shiyyar manyan tekuna ta kasa da kasa wato (ICGLR), da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen tsakiyar Afrika ta (ECCAS), da kungiyar tarayyar Afrika (AU), dukkansu sun yi maraba da yadda zaben ya gudana, duk kuwa da ’yan kura-kuran da aka samu.